Yan bindiga sun bindige Dansanda yayin rakiyar sakamakon zabe

Yan bindiga sun bindige Dansanda yayin rakiyar sakamakon zabe

Wasu gungun yan bindiga sun halaka jami’in dansanda mai mukamin kofur dake aikin bayar da tsaro ga sakamakon zabe tare da yi musu rakiya daga karamar hukumar Ipokia zuwa cibiyar tattara sakamakon zabe dake garin Ilaro na jahar Ogun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, 24 ga watan Feburairu da misalin karfe 8:30 na dare, a daidai unguwar Eredo dake cikin karamar hukumar Yewa ta kudu.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An banka ma ofishin INEC wuta, an sace baturen zabe

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun yi ma ayarin wakilan zabe, ma’aikatan zabe da Dansanda kwantan bauna ne, inda daga lokacin da suka hangensu suka bude ma motar dake jigilarsu wuta.

Kaakakin rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni kwamishinan Yansandan jahar, Ahmed Iliyasu ya bada umarni ga mataimakinsa wanda ke kula da bincike da tattara bayanai a rundunar, daya kaddamar da bincike akan lamarin.

Daga karshe Abimbola ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan lamari, amma ya bada tabbacin zasu damko wuyar duk wasu masu hannu cikin aikata mummunan aikin, kuma yace zasu tabbata sun fuskanci hukuncin daya dacesu.

A wani labarin kuma, gungun miyagun mutane dauke da muggan makamai sun kai farmaki zuwa babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, dake karamar hukumar Orlu ta jahar Imo, yankin da gwamnan jahar Rochas Okorocha ya fito.

A ranar Lahadi ne Yan bindigan suka yi awon gaba da babban jami’in zabe na karamar hukumar, Mista December Aloy Njoku tare baturen zabe dake tattara sakamakon zaben Sanata na mazabar Orlu, zaben da aka ruwaito Rochas ya lashe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel