Sakamako: Atiku ya bawa Buhari ratar kuri’u fiye da 300,000 a Enugu

Sakamako: Atiku ya bawa Buhari ratar kuri’u fiye da 300,000 a Enugu

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwa jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kayar da abokin takarar sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, na jam’iyyar APC a jihar Enugu.

A sakamakon zaben jihar ta Enugu, Buhari ya samu kuri’u 54,423, yayin da Atiku ya samu kuri’u 355,553.

An kada jimillar kuri’u 451,063 a jihar Enugu, an samu kuri’u 30,049 da su ka lalace.

Sai dai a jihar Yobe da ke rewa maso gabashin Najeriya, sakamakon da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar a matakin kujerar shugaban kasa ya nuna cewar jam’iyyar APC mai mulki ta samu kuri’u 497,914 yayin da jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 50,763 kacal a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Baturen zaben kujerar shugaban kasa a jihar Yobe, Farfesa Abubakar Gundiri, ne ya sanar da sakamakon da aka kammala tattara wa daga kananan hukumomi 17 da jihar ke da su. Ya sanar da sakamakon zaben ne yau, Lahadi, a gidan gwamatin Yobe da ke Damaturu, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewar jihar Yobe na adadin ma su kada kuri’a 1,365,913, wanda daga cikin su aka tantance adadin mutane 601,059 da su ka yi zabe a ranar Asabar.

Farfesa Gundiri ya ce an kada jimillar kuri’u 586,137, wanda daga ciki jamm’iyyar APC ta samu kuri’u 497,914, yayin da jam’iyyar PDP ta samu adadin kuri’u, 50,763.

A cewar baturen zaben, an samu jimillar kuri’u ingantattu 559,365, yayin da aka samu kuri’u 26,772 da su ka lalace.

Yay aba wa ma su zabe, ma su ruwa da tsaki da wakilan jam’iyyu bisa hadin kan da su ka bayar wajen ganin an gudanar da zabe cikin lwanciyar hankali da lumana a jihar.

Kazalika, wakilan jam’iyyun APC, Dakta Zaji Bunu, da na PDP, Dakta Abdu Bulama, sun amince da sakamakon zabe kuma sun rattaba hannu a kan takardar sakamakon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel