Na godewa mutanen da su ka zabe ni komai runtsi a Kaduna – Shehu Sani

Na godewa mutanen da su ka zabe ni komai runtsi a Kaduna – Shehu Sani

Bisa dukkan alamu Sanatan Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya ga alamu cewa ba zai ci zaben da aka yi ba. Tuni dai ‘Dan majalisar ya fara yi wa Duniya jawabi yana dinbin godiya ga mutanen sa.

Na godewa mutanen da su ka zabe ni komai runtsi a Kaduna – Shehu Sani
Shehu Sani ya jarraba farin jinin sa a jam'iyyar PRP
Asali: UGC

A wani sako na musamman da ‘Dan majalisar ya fitar a kafafen yada labarai na zamani, mun ji labari cewa Sanatan ya nuna godiya ga daukacin al’ummar da su ka zabe sa a karkashin sabuwar jam’iyyar sa ta PRP mai adawa.

Sanatan yake cewa ya tsaya ne da kafafun karan kan-sa ba wai ya labe a bayan wani bane domin mutane su zabe sa. Sani yana ganin cewa duk wanda ya kada masa kuri’a, ya zabe sa ne domin ganin cewa shi ne ya dace.

KU KARANTA: Sakamakon zaben shugaban kasa da 'Yan Majalisa a Kaduna

Kwamared Shehu Sani ya nuna cewa ko da ya sha kasa a zaben majalisa da aka yi a karshen makon da ya gabata, bai ji kunyar tsayawa tsayin daka da yayi shi kadai a jam’iyyar sa ba, ba kuma tare da rabawa mutane abin Duniya ba.

Sanatan na Kaduna ta tsakiya mai-ci, Shehu Sani, ya sauya-sheka ne daga jam’iyyar APC zuwa PRP mai adawa bayan ya gagara samun tikitin takara a jam’iyyar mai mulki domin ya samu zarcewa a majalisar dattawa a 2019.

A zaben da aka yi kwanan nan, kun ji Sanatan ya sha kasa a akwatin da yayi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya a cikin Unguwar Sarki a cikin jihar Kaduna. Jam’iyyar sa ta PRP ta samu 51 ne inda APC ta samu 236.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel