PDP na shirya magudi a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu – Buba Marwa

PDP na shirya magudi a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu – Buba Marwa

A jiya, Lahadi, ne Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa (INEC) da jami’an tsaro da su dakatar da jam’iyyar adawa ta PDP daga yunkurin shirya magudi a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu.

Da ya ke Magana da manema a garin Yola, Marwa ya zargi PDP da yunkurin tayar da rikici domin samun damar canja sakamako zabe bayan sun fahimci cewar jama’a ba su zabi dan takarar su ba.

Ya yi kira ga INEC da jami’an tsaro da su sa ka ido a cibiyoyin tattara sakamako domin ganin ba a yi wani abu da ya saba wa ka’ida.

Marwa, shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari a tsakanin mata da matasa, ya bukaci ‘yan jam’iyyar APC da su kula sosai don ganin cewar jam’iyyar adawa ba ta samu damar yin magudi ba.

PDP na shirya magudi a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu – Buba Marwa
Buba Marwa
Asali: UGC

Korafin na Marwa na zuwa ne a daidai lokacin da Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya tsawatar wa jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC domin ganin ba su kawo rudani a cibiyoyin tattara sakamakon zaben ba.

A wani jawabi da mai taimaka ma sa a bangaren yada labarai, Mista Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa yadda su ka yi tururuwa wajen fito wa domin kada ma sa kuri’a a zaben da aka yi jiya, Asabar, 23 ga watan Fabarairu.

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Buhari ya yi wa Atiku raga-raga a jihar Yobe

Ina mika godiya ga miliyoyin ‘yan Najeriya bisa yadda su ka yi tururuwar fito wa domin kada min da jam’iyya ta kuri’un su, ba tare da sun daga zaben da aka yi ya kasha ma su jiki ba.

“Kuri’u ma fi rinjaye da za mu samu daga yankin kudu maso gabas, kudu maso kudu da karin adadin kuri’un da za mu samu daga kudu maso yamma da arewa ta tsakiya, mu na da tabbacin cewar PDP za ta samu nasara.

"Mu na sa ran sanar da ku labara mai dadi daga ragowar sassan Najeriya nan ba da dadewa ba.

Mu na kira da jama’ar Najeriya d su kwantar da hankalim su domin kwanan nan za su yi bankwana da wahalar da su ka shafe hekaru hudu su na sha,” a cewar Atiku.

Atiku ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara sa-ido a cikin sa’o’i 48 domin kare kuri’un su da su kada a akwatinan sun a zabe tare da yin zargin cewar jam’iyyar APC na kokarin shirya magudi a cibiyoyin tattara sakamako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel