Saraki ya karyata batun taya zababben sanatan APC murna

Saraki ya karyata batun taya zababben sanatan APC murna

Yusuph Olaniyonu, hadimin shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya musanta rahotanni dake cewa mista Saraki ya taya Ibrahim Oloriegbe wanda ya lashe kujeran majalisa a zaben da aka gudanar murna.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Mista Oloriegbe, dan takaran jam’iyyar APC wanda yayi takara da Mista Saraki a zaben Majalisan Tarayya a ranar Asabar ne ya lashe zaben yankin Kwara ta Tsakiya.

Mista Olaniyonu a wani jawabi da ya gabatar a ranan Litinin, 25 ga watan Fabrairu, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su ki amincewa da rahoton dake ikirarin cewa Saraki ya amince da sakamakon zabe.

Saraki ya karyata batun taya zababben sanatan APC murna
Saraki ya karyata batun taya zababben sanatan APC murna
Asali: Depositphotos

Yace: “Za a bayyana matsayin Saraki ga al’umma da yammacin yau Litinin.”

“Al’umma su yi watsi da kagaggen jawabai da ake yadawa a shafin zumunta na whatsapp.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya share kananan hukumomi 32 a Kano

"A yammacin yau zamu bayyana muku matsayinmu akan zaben da aka gudanar."

Yace, “Jam’iyyar APC su daina gabatar da jawabai dake nunawa kansu murna wanda suke alakantawa da sansanin mu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel