Zaben 2019: Atiku ya tika Buhari da kasa a garin Abuja

Zaben 2019: Atiku ya tika Buhari da kasa a garin Abuja

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta tabbatar da nasarar dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a garin Abuja bayan babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

A sakamakon zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar ta makon da ya gabata, hukumar zabe ta kasa ta tabbatar da nasarar Atiku a garin Abuja, bayan kammala kididdiga da tantance kuri'u.

Kai tsaye daga hedikwatar hukumar INEC, yadda sakamakon zaben shugaban kasa ya kaya a garin Abuja
Kai tsaye daga hedikwatar hukumar INEC, yadda sakamakon zaben shugaban kasa ya kaya a garin Abuja
Asali: UGC

Majiyar jaridar Legit da ke reshen garin Abuja ta tabbatar da cewa, Atiku da ya kasance dan takara na jam'iyyar adawa ta PDP ya yi nasara da kimanin kuri'u 259,997.

Fashin baki na sakamakon zaben kamar yadda hukumar INEC ta bayyana ya tabbatar da cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya gaza kawo majalisi na fadar sa yayin da lashe kuri'u 152,224 kacal.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Gamayyar kuri'u da tsohon mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya samu na kuri'un al'umma ya tabbatar ta nasarar a garin Abuja. Kazalika hukumar hasashe na nuni da cewa zai yi nasara a mahaifar sa da ta kasance jihar Adamawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel