Zan jira har INEC ta kaddamar da sakamakon karshe - Buhari

Zan jira har INEC ta kaddamar da sakamakon karshe - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 25 ga watan Fabrairu yace shi bai yarda da jita-jita ba sannan cewa ya gwammaci ya jira sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta kaddamar.

Ana dai ta watsa sakamako daban-daban a kafofin sada zumunta akan zaben Shugaban kasa nay an majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Sai dai a lokacin da shugaba Buhari ya isa filin jirgin Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja a ranar Litinin, ya bayyana cewa zai jira sakamakon karshe daga bakin INEC.

Zan jira har INEC ta kaddamar da sakamakon karshe - Buhari
Zan jira har INEC ta kaddamar da sakamakon karshe - Buhari
Asali: Depositphotos

Buhari ya bar Abuja ne a ranar Juma’ a zuwa Daura, jihar Katsina inda a han ne ya sauke hakkin da ya rataya a wuyansa a matsayin dan kasa na kada kuri’ a.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Surukin Ganduje ya sha kasa a zaben Sanata

A baya Legit.ng ta rahoto cewa sakamakon zabe da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar a matakin kujerar shugaban kasa ya nuna cewar jam’iyyar APC mai mulki ta samu kuri’u 497,914 yayin da jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 50,763 kacal a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Baturen zaben kujerar shugaban kasa a jihar Yobe, Farfesa Abubakar Gundiri, ne ya sanar da sakamakon da aka kammala tattara wa daga kananan hukumomi 17 da jihar ke da su.

Ya sanar da sakamakon zaben ne yau, Lahadi, a gidan gwamatin Yobe da ke Damaturu, babban birnin jihar. Ya bayyana cewar jihar Yobe na adadin ma su kada kuri’a 1,365,913, wanda daga cikin su aka tantance adadin mutane 601,059 da su ka yi zabe a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel