Babbar magana: Jami'in tattara sakamakon zabe ya yi yunkurin guduwa, an cafke shi

Babbar magana: Jami'in tattara sakamakon zabe ya yi yunkurin guduwa, an cafke shi

An kai ruwa rana a wani abu da ake kallo a matsayin 'abu kamar wasa' a karamar hukumar Bokos, jihar Filato, a yayin da jami'in INEC mai tattara sakamakon zaben jihar, Farfesa Musa Izam na jihar Jos, ya yi yunkurin tserewa ba tare da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka kada a ranar Asabar a jihar.

Jami'in hukumar, ya nemi a uzirin fita daga wajen daga wajen jami'an jam'iyyu, a lokacin da ake kan tattara sakamakon zaben, da nufin zai shiga makewayi.

Shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Bokkos, Mr Michael Abi, ya ce sai da aka kammala kawo sakamakon zaben gundumomi 12 da ke karamar hukumar, ana jiran jami'in hukumar ya sanar da sakamakon, a nan ne ya nemi a bashi lokaci domin ya kewaya bandaki.

KARANTA WANNAN: Sakamakon zaben jihohi: PDP ta samu nasarar lashe zaben jihar Adamawa

Babbar magana: Jami'in tattara sakamakon zabe ya yi yunkurin guduwa, an cafke shi
Babbar magana: Jami'in tattara sakamakon zabe ya yi yunkurin guduwa, an cafke shi
Asali: Original

Ya ce: "Sai dai ba mu gamsu da wannan uzirin na sa ba, domin haka muka umurci mutanenmu akan su sanya masa idanu. Kuma kamar yadda muka yi hasashe, sai muka hango jami'in ya shiga wata mota, ya tsere daga cibiyar tattara sakamakon.

"Ba tare da mun bata lokaci ba muka bi bayansa cikin matsanancin gudu har zuwa kan titin karamar hukumar Barikin Ladi zuwa Jos, inda muka cimmasu a Maikatako kusa da kauyen Kuba a Bokkos.

"Sai dai babban abun mamakin shine yadda muka same shi tare da wani babban mai tallafawa gwamna Simon Lalong ta fuskar tsaro a cikin motar, ba dai za mu fadi sunan mai tallafawa gwamnan ba a halin yanzu.

"Mun dawo da shi cibiyar tattara sakamakon zaben, domin ya baiwa dukkanin mutanen da ke cikin zauren hakuri akan wannan danyen aiki da ya yi."

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Antoni-Janar kuma kwamishinan shari'a, Mr Jonathan Mawuyau, ya kuma baiwa jama'a hakuri a madadin Farfesan, yana mai bukatar da aci gaba da tattarawa tare da fadin sakamakon zabukan gundumomin karamar hukumar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel