Da dumi dumi: An banka ma ofishin INEC wuta, an sace baturen zabe

Da dumi dumi: An banka ma ofishin INEC wuta, an sace baturen zabe

Wasu gungun miyagun mutane dauke da muggan makamai sun kai farmaki zuwa babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, dake karamar hukumar Orlu ta jahar Imo, yankin da gwamnan jahar Rochas Okorocha ya fito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi awon gaba da babban jami’in zabe na karamar hukumar, Mista December Aloy Njoku tare baturen zabe dake tattara sakamakon zaben Sanata na mazabar Orlu, zaben da aka ruwaito Rochas ya lashe.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi awon gaba da matasan NYSC guda 18 a Akwa Ibom

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Feburairu, inda a ranar kuma aka samu wasu bata gari suka banka ma ofishin INEC dake karamar hukumar Isiala Mbano na jahar ta Imo, sai dai ba haka banza lamarin ya auku ba.

Majiyarmu ta tabbata da cewa an samu wannan matsala ne jim kada bayan jami’an biyu sun dakatar da sanar da sakamakon zaben daya gudana a kananan hukumomin jahar guda goma sha daya cikin goma sha biyu dake mazabar, bayan sun fahimci akwai yan matsaloli tattare da sakamakon.

Gwamnan jahar, Okorocha shine dan takarar Sanatan APC na mazabar, yayin da Jones Onyereri ke takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, sai dai a sanadiyyar wannan tsaiko da aka samu ta sa kwamishinan INEC na jahar ya bada umarnin dakatar da sanarwar.

Bugu da kari, kwamishinan zaben, Farfesa Francis Chukwuemeka ya umarci jami’an biyu su gurfana a gabansa domin tsatstsage masa bayanai a babban ofishin hukumar dake garin Owerri, inda suna kan hanyarsu ta amsa gayyatar ne aka yi musu kwantan bauna, aka yi awon gaba dasu.

Kaakakin hukumar INEC ta jahar, Emmanuella Okpara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace shugaban hukumar ya dakatar da sanarwar sakamakon zaben ne saboda ya samu labarin ana tilasta musu su karanta sakamakon zabe na bogi ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel