Ban taba fafatawa a zabe da na sha wahala kamar bana ba —Abdulmumin Jibrin

Ban taba fafatawa a zabe da na sha wahala kamar bana ba —Abdulmumin Jibrin

- Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilan kasar, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa bai taba fafatawa a zaben da ya sha wahala kamar na 2019 ba

- Abdulmumin ya mika godiya ga Allah akan nasarar da ya sake yi a karo na uku

- Ya ce a zai sake takarar kujerar majalisar tarayya ba

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilan kasar, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa bai taba fafatawa a zaben da ya sha wahala kamar na shekarar 2019 ba.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter don mika godiya ga Allah kan nasarar da ya samu ranar Lahadi, Abdulmumin ya ce ba zai sake tsayawa takarar majalisar wakilai ba.

Ban taba fafatawa a zabe da na sha wahala kamar bana ba —Abdulmumin Jibrin
Ban taba fafatawa a zabe da na sha wahala kamar bana ba —Abdulmumin Jibrin
Asali: Depositphotos

"Mun yi nasara duk da tarin kalubalen da muka fuskanta. Ban taba shiga zabe da na sha wuya kamar wannan ba. Na kusa durkusawa. Wannan shi ne fadan karshe mai matukar taba zyuciya saboda ba zan sake tsayawa takarar majalisar tarayya ba," Cewar Abdulmumin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rochas Okorocha kujerar Sanatan Imo ta yamma

Kafin zabe Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a, 22 ga watan Fabrairu ta kama wani mamba na majalisar wakilai mai wakiltan Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, kan harin da aka kai wa tawagar tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso.

Wasu da ake zargin yan daba ne magoya bayan dan majalisar ne suka kai hari ga ayarin Kwankwaso. Anyi zargin cewa yan iskan sun yi wata hanya zuwa kauyen Kofa kawanya sannan suka yi yunkurin hana masu wucewa bi ta kauyen.

Akalla mutane biyar aka kashe, yayinda wasu da dama suka ji rauni lokacin da bangarorin biyu suka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel