Sakamakon zabe: Atiku ya baiwa Buhari tazara a jihar Filato

Sakamakon zabe: Atiku ya baiwa Buhari tazara a jihar Filato

Rahotannin da Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, na ci gaba da samun nasarar zaben shugaban kasa da aka kad'a a jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa, zuwa yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 13 na jihar.

Haka zalila, kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ta ruwaito cewa hukumar INEC na kan jiran isowar sakamakon zaben kananan hukumomi hudu na jihar. Farfesa Richard Kimbir, jami'in tattara sakamako na jihar, ya bayyana Atiku a matsayin wanda ya lashe zabe a kananan hukumomi 10.

Shehu ya ce dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC Muhammadu Buhari, ya lashe zabe a kananan hukumomi ukku kawai.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dira birnin tarayya Abuja

Sakamakon zabe: Atiku ya baiwa Buhari tazara a jihar Filato
Sakamakon zabe: Atiku ya baiwa Buhari tazara a jihar Filato
Asali: Depositphotos

NAN ta ruwaito cewa PDP ta lashe zabe a Jos ta Kudu, Bokkos, Barkin Ladi, Riyom, Bassa, Langtang ta Arewa da ta Kudu, Pankshin, Mikang da kuma Kanke.

Kambir ya ce jam'iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomin Jos ta Gabas, Shendam da kuma Qua'anpan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel