Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dira birnin tarayya Abuja

Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dira birnin tarayya Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya je Daura, jihar Katsina domin kad'a kuri'arsa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, ya dira birnin tarayya Abuja a yau Litinin, 25 ga watan Fabreru, 2019.

Buhari, wanda ya bar unguwarsa ta GRA a Daura, ya shiga jirgi mai saukar ungulu da misalin karfe 10 na safiya, inda ya dira filin sauka da tashi na jiragen sama na Umaru Yar'Adua da ke Katsina da misalin karfe 10:25 na safiya.

KARANTA WANNAN: Sakamakon zabe: Buhari ya baiwa Atiku tazara mai nisa a Yobe da Nasarawa

Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dira birnin tarayya Abuja
Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dira birnin tarayya Abuja
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasar ya bar Katsina da misalin karfe 10:47 na safiya, cikin jirgin sama da aka warewa shugaban kasar.

Idan ba a manta ba, shugaban kasar ya isa Katsina a ranar Juma'ar da ta gabata, domin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel