Yanzu Yanzu: Surukin Ganduje ya sha kasa a zaben Sanata

Yanzu Yanzu: Surukin Ganduje ya sha kasa a zaben Sanata

Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya fadi zaben dan takarar Sanata a Kudu maso yammacin jihar.

A sakamakon zabe wanda jami’ in zabe a yankin Oyo ta Kudu, Farfesa Wole Akinsola ya fitar, Dr Kola Balogun na jam’ iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne ya lashe zaben inda ya kayar da Ajimobi na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma sanata mai ci Sanata Adesoji Akanbi na jam’ iyyar African Democratic Congress (ADC).

Mista Ajimobi, wanda shi ne gwamna mai ci na jam'iyar APC ya samu kuri'a 92,218, yayinda wanda ya lashe zaben Balogun na PDP ya samu kuri'a 105,716.

Yanzu Yanzu: Surukin Ganduje ya sha kasa a zaben Sanata
Yanzu Yanzu: Surukin Ganduje ya sha kasa a zaben Sanata
Asali: Depositphotos

Gwamna Ajimobi shi ne surukin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda dansa Idris Ajimobi ya auri Fatima Ganduje.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rochas Okorocha kujerar Sanatan Imo ta yamma

A wani lamari makamancin haka mun ji cewa Mohammed Sani Musa na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben kujerar Sanata a yankin Niger ta gabas a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Da yake sanar da sakamakon zaben a Minna a ranar Litinin, 25 ga watan Fabrairu, jami’ in zaben, Farfesa Ali Audu Jega yace Musa ya samu kuri’u 229,415 inda abokin adawarsa na PDP, Ishaku Ibrahim ya samu 116,143.

Dan takarar jam’ iyyar ADC, Musa ya samu kuri’ u 2,655.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel