Sakamakon zabe: Buhari ya baiwa Atiku tazara mai nisa a Yobe da Nasarawa

Sakamakon zabe: Buhari ya baiwa Atiku tazara mai nisa a Yobe da Nasarawa

Bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, jami'an tattara sakamakon zabe na hukumar INEC da ke cibiyoyin tattara sakamakon zaben na jihohin Nasara, Adamawa da Yobe, sun bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, kamar haka:

JIHAR NASARAWA

A karon farko, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zabe a jihar Nasarawa tun bayan fara kaddamar da yakin zabensa a shekarar 2003, wanda ya bashi damar lallasa dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, dan tazarar kuri'u 37,896.

Sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a garin Lafia ta sanar, ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya samu kuri'u 279,315, yayin da Atiku ya samu kuri'u 241,419.

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: INEC ta bayyana APC a matsayin wacce ta lashe sanatan Osun ta tsakiya

Buhari ya samu nasara a kananan hukumo 8 yayin da Atiku ya samu nasara a kananan hukumo 5, wanda ya bayyana faduwar PDP a karon farko a jihar Nasarawa a zaben shugaban kasa tun bayan fara demokaradiya a 1999.

JIHAR YOBE

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari, na kan gaba a jihar Yobe, wanda ya bashi damar lallasa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u 418,851, a zaben ranar Asabar da ya gudana.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar INEC da ke tattara sakamakon zabe a kananan hukumomi 16 na jihar, a gaban babban jami'in tattara sakamakon zaben na jiha, Farfesa Abubakar Gunduri, APC ta samu kuri'u 466,439 yayin da PDP ta samu kuri'u 47,583.

A wani labarin kuwa:

Sanata Abdullahi Adamu na jam'iyyar APC, ya samu nasarar lashe zaben kujerar sanatan mazabar Nasarawa ta Yamma, bayan samun kuri'u 115,298 a zaben da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Adamu, wanda tsohon gwamnan jihar ne, ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Alhaji Bala Ahmed Aliyu, wanda ya samu kuri'u 85,615, wanda ya bashi damar komawa majalisar dattijai a karo na ukku.

Jami'in tattara sakamakon zabe na mazabar, Farfesa Ahmed Yakubu ya bayyana hakan a Keffi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel