Yanzu Yanzu: Rochas Okorocha ya lashe kujerar Sanatan Imo ta yamma

Yanzu Yanzu: Rochas Okorocha ya lashe kujerar Sanatan Imo ta yamma

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya lashe zaben kujerar sanata a yankin Imo ta Yamma

- Okocha ya samu kuri’u 97,762 yayinda babban abokin adawarsa na jam’iyyar PDP Jones Onyereri ya samu kuri’u 63,117

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya lashe zaben kujerar sanata a yankin Imo ta Yamma, a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Jami’in zabe, farfesa Ibeawuci Francis, ya bayyyana Okorocha a matsayin wanda yayi nasara bayan ya samu kuri’u 97,762 inda ya ba babban abokin adawarsa dake a jam’iyyar PDP Jones Onyereri wanda ya samu kuri’u 63,117 kashi.

Yanzu Yanzu: Rochas Okorocha kujerar Sanatan Imo ta yamma
Yanzu Yanzu: Rochas Okorocha kujerar Sanatan Imo ta yamma
Asali: UGC

Mohammed Sani Musa na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben kujerar Sanata a yankin Niger ta gabas a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

Da yake sanar da sakamakon zaben a Minna a ranar Litinin, 25 ga watan Fabrairu, jami’ in zaben, Farfesa Ali Audu Jega yace Musa ya samu kuri’u 229,415 inda abokin adawarsa na PDP, Ishaku Ibrahim ya samu 116,143.

Dan takarar jam’ iyyar ADC, Musa ya samu kuri’ u 2,655.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel