Yanzu-yanzu: Buhari ya tashi daga Daura, zai koma Abuja

Yanzu-yanzu: Buhari ya tashi daga Daura, zai koma Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga mahaifarsa, Daura, jihar Katsina domin komawa aiki a babban birnin tarayya Abuja.

Buhari ya bar Duara ne bayan ganawa da tawagar mai martaba sarkin Daura, Umar Farouq, da safiyar Litinin, 25 ga watan Febrairu, 2019.

Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari na barin gidansa yanzu a Daura, jihar Katsina domin komawa Abuja, bayan kada kuri'arsa ranar Asabar."

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya koma birnin tarayya Abuja bayan kada kuri'arsa a mazabarsa dake Yola, jihar Adamawa a ranan Lahadi.

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya lallasa Alhaji Atiku Abubakar ya a rumfar zabensa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel