Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa yayi nasara a zaben 2019

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa yayi nasara a zaben 2019

- Sanata Ekweremadu yayi nasara a zaben Majalisar Dattawa a karkashin PDP

-Ike Ekweremadu ya samu kuri’a 86,088 inda ya kada Juliet Ibekaku-Nwagwu

- Babban ‘Dan Majalisar yana shirin zama Sanata a karo na 5 kenan a Najeriya

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa yayi nasara a zaben 2019
Sanata Ike Ekweremadu yana da sauran taliya a Majalisar Dattawa
Asali: Original

Sanata Ike Ekweremadu na jam’iyyar adawa ta PDP ya lashe zaben ‘dan majalisar dattawa na yankin Enugu ta yamma inda ya doke ‘yar takarar jam’iyyar APC Juliet Ibekaku-Nwagwu, kamar yadda aka sanar dazu da tsakar dare.

Ike Ekweremadu ya samu kuri’a 86, 088 a zaben da aka yi shekaran jiya, yayin da babbar abokiyar hamayyar sa kuma watau Juliet Ibekaku-Nwagwu ta jam’iyyar APC ta biyo bayan sa da kuri’u 15, 187 inji hukumar zabe na INEC.

KU KARANTA: Sanata Dino Melaye zai sake komawa Majalisar Dattawa

Babban jami’in INEC na wucin-gadi da ya tattara zaben yankin, watau Farfesa Douglas Nwabueze, shi ne ya bayyana cewa Sanata Ike Ekweremadu ne yayi nasara a zaben mazabar yammacun Enugu, a madadin hukumar INEC.

Sanata Ike Ekweremadu wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar a halin yanzu, ya godewa mutanen sa da su ka sake zaben sa a wannan karo domin ya wakilce su a karo na 5 a majalisar tarayyar Najeriya.

Ekweremadu yayi alkawari cewa ba zai sake ya ba al’ummar sa kunya ba. Sanatan ya kuma sha alwashin cewa zai saka masu da irin alherin da su kayi masa. Yanzu haka dai Bukola Saraki wanda shi ne shugaban majalisar, ya rasa kujerar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel