Yanzu Yanzu: APC ta lashe zaben Sanata a yankin Niger ta gabas

Yanzu Yanzu: APC ta lashe zaben Sanata a yankin Niger ta gabas

Mohammed Sani Musa na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben kujerar Sanata a yankin Niger ta gabas a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Da yake sanar da sakamakon zaben a Minna a ranar Litinin, 25 ga watan Fabrairu, jami’ in zaben, Farfesa Ali Audu Jega yace Musa ya samu kuri’u 229,415 inda abokin adawarsa na PDP, Ishaku Ibrahim ya samu 116,143.

Dan takarar jam’ iyyar ADC, Musa ya samu kuri’ u 2,655.

Yanzu Yanzu: APC ta lashe zaben Sanata a yankin Niger ta gabas
Yanzu Yanzu: APC ta lashe zaben Sanata a yankin Niger ta gabas
Asali: Facebook

Jega yace: “Mohammed Sani Musa na APC ya cika dukkanin abubuwan da doka ta bukata sannan ya samu kuri’u mafi yawa, don aka an kaddamar dasi a matsayin wanda yayi nasara a zaben.”

A wani lamari makamancin wannan, Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Hassan a matsayin wanda yayi nasara a zaben yan majalisa a yankin Arewa maso gabashin jihar.

KU KARANTA KUMA: APC ta lashe dukkanin kujerun sanata a Kwara

Mista Hassan, wanda ya kasance dan takara a jam’iyyar APC, ya samu kuri’u 184,185 inda ya kayar da sanatan PDP mai ci, Ubale Shittu, wanda ya samu kuri’u 103,039.

Da wannan bayanin ne, jam’iyyar APC ta yi nasaran lashe zabe a dukkanin yankin Arewa maso gabashin Jigawa, wanda ke dauke da kananan hukumomi guda bakwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel