Yanzunnan: APC ta lashe zaben sanatan Osun ta tsakiya - INEC

Yanzunnan: APC ta lashe zaben sanatan Osun ta tsakiya - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APC, Dr Ajibola Bashiru a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanatan Osun ta tsakiya. Haka zalika Mrs Taiwo Oluga ta lashe zaben mazabar Ayedaade/Irewole/Isokon a majalisar wakilan tarayya.

Jami'in tattara sakamakon zabe a mazabar, Farfesa Titilayo Adelaje daga jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, ya bayyana Ajibola a matsayin wanda ya lashe zaben bayan samun kuri'u 132,821, wanda ya bashi damar lallasa dan takarar PDP, Alhaji Ganiyu Olaoluwa wanda ya samu kuri'u 106,779.

KARANTA WANNAN: Sanata Stella Oduah ta ci zaben Sanatar Anambra ta Arewa da kuri'u 113,989

Yanzunnan: INEC ta bayyana APC a matsayin wacce ta lashe sanatan Osun ta tsakiya
Yanzunnan: INEC ta bayyana APC a matsayin wacce ta lashe sanatan Osun ta tsakiya
Asali: UGC

INEC ta kuma bayyana Mrs Taiwo Oluga a matsayin wacce ta lashe zaben kujerar majalisar wakilan tarayya a mazabar Ayedaade/Irewole/Isokon karkashin jam'iyyar APC.

Jami'in tattara sakamakon mazabar, Farfesa Bamidele Solomon ya bayyana cewa Oluga ta samu kuri'u 36,876 yayin da mai takara a PDP ya samu kuri'u 31,956.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel