APC ta lashe dukkanin kujerun sanata a Kwara

APC ta lashe dukkanin kujerun sanata a Kwara

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe dukkanin kujeru uku na zaben yan majalisa a jihar Kwara da aka gudanar a ranar Asabar da ya gabata.

Sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar ta bayyana cewa jam’iyyar APC ta yi nasara a yankin Kudancin Kwara, Arewacin Kwara da yankin Kwara ta tsakiya.

Legit.ng ta rahoto a baya yanda Shugaban majalisan dattawa Bukola Saraki ya rasa kujerar shi a yankin Kwara ta tsakiya inda Ibrahim Oloriegbe dake jam’iyyar APC ya lashe zaben.

A Arewacin Kwara, jam’iyyar APC ta samu kuri’u 98170 inda ta kayar da jam’iyyar PDP wacce ta samu kuri’u 33,364.

APC ta lashe dukkanin kujerun sanata a Kwara
APC ta lashe dukkanin kujerun sanata a Kwara
Asali: UGC

Dan takaran jam’iyyar APC, Umar Sadiq ne ya lashe zaben kujerar majalisar.

Adadin masu zabe da suka yi rijista sun kai 386,969 sannan yawan kuri’u da aka kada sun kai 137,456. Kuri’u da aka ki sun kai 4,544 sannan kuri’u masu inganci sun kai 132,912.

A yankin Kudancin Kwara, Lola Ashiru na jam’iyyar All Progressives Congress ne yayi nasar lashe zabe.

Jami’in zabe, Sylvia Malomo, yayin bayyana sakamakon zaben a karamar hukumar Irepodun a Omu-Aran, ya ce Ashiru ya samu kuri’u 89,704 inda ya lashe zaben.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Atiku na gaba da Buhari a Benue inda ya lashe 7 daga cikin kananan hukumomi 11

Abokin adawansa Rafiu Ibrahim dake a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya samu kuri’u 45,176.

Mista Ibrahim ya kasance shugaban kwamiti kan harkokin bankuna.

Yawan masu zabe wadanda suka yi rijista a yankin sun kai 432,499, tare da kuri’u masu inganci guda 136,889. Yawan kuri’u da aka ki sun kai 3,119 sannan kuri’u da aka kada sun kai 140,006.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel