Yan bindiga sun yi awon gaba da matasan NYSC guda 18 a Akwa Ibom

Yan bindiga sun yi awon gaba da matasan NYSC guda 18 a Akwa Ibom

Akalla ma’aikatan zabe na wucin gadi masu yi ma kasa hidima na NYSC guda goma sha takwas ne yan bindiga suka yi garkuwa dasu a jahar Akwa Ibom a yayin da ake gudanar da zabukan 2019 a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan INEC na jahar Akwai Ibom Mike Igini ne ya tabbatar da haka a yayin yake ganawa da manema labaru a garin Uyo, inda yace an sace ma’aikatan ne a sassa daban daban na jahar.

KU KARANTA: Ministan Buhari ta lashe kujerar dan majalisar tarayya a Yobe

Sai dai Mista Igini yace sun samu sa’an ceto wasu daga cikin yan bautan kasa da taimakon jami’an tsaro, haka zalika wani Malamain jami’ar Uyo, Mista Kufre Etuk yaci dan banzan duka a hannun wasu yan baranda a karamar hukumar Urun.

Da kyar Malamin ya tsere daga hannun yan daban, inda ya samu mafaka a cikin wani kungurmin daji, bai fito ba sai da gari yaw aye, bugu da kari wasu yan daban sun lalata kayan zabe na mazabu goma dake cikin karamar hukumar Ikono, duk a Akwa Ibom.

A jawabinsa, kwamishina Igini yace “Duba da munana rahotannin da muka samu na tashe tashen hankula, satar kayan zabe, shirya sakamakon zabe na bogi, garkuwa da ma’aikatan zabe, don haka dole ne mu dauki mataki.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kashe wakilan zabe na jam’iyyar APC guda biyar a wani harin kwantan bauna da suka kai musu a ranar Lahadi, 24 ga watan Feburairu, kamar yadda rundunar Yansandan jahar Taraba ta tabbatar.

Yan bindigan sun kashe wakilan jam’iyyar na APC ne da tsakar daren Lahadi yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida a karamar hukumar Karim Lamido, inda suka gudanar da aikin sa ido a zaben da aka yi.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, David Misal ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace mutanen biyar sun fito ne daga kauyen Umari akan hanyarsu ta zuwa kauyen Cambri, duk a cikin karamar hukumar Karim Lamido a lokacin da aka kai musu harin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel