Sakamakon Zabe: Buhari ya lashe zaben karamar hukumar farko a jihar Adamawa

Sakamakon Zabe: Buhari ya lashe zaben karamar hukumar farko a jihar Adamawa

A yayin da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019 ke ci gaba da bayyana, mun samu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasara a karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa.

Sakamakon Zabe: Buhari ya lashe zaben karamar hukumar farko a jihar Adamawa
Sakamakon Zabe: Buhari ya lashe zaben karamar hukumar farko a jihar Adamawa
Asali: Twitter

Duk da kasancewar jihar Adamawa mahaifa ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shugaban kasa Buhari da ya kasance dan takara na jam'iyyar APC ya fara samun nasara yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta shiga fidda sakamakon jihar.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya lashe kuri'u 17,765 yayin da abokin adawar sa Atiku ya samu kuri'u 14,673 kacal a karamar hukumar Gerie ta jihar Adamawa.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu ana ci gaba da kirdadon sakamakon sauran kananan hukumomi yayin da jihar Adamawa ta ke kunshe da kananan hukumomi 22.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan mun samu cewa, a yayin da 'yar takarar kujerar Sanatan shiyyar Adamawa ta Arewa, Sanata Binta Masi ta jam'iyyar APC ta samu kuri'u 63,219, ta sha babban kaye a hannun dan takara na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 79,337.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel