2019: Dino Melaya ya doke Smart Adeyami a Kogi ta Yamma

2019: Dino Melaya ya doke Smart Adeyami a Kogi ta Yamma

Mun ji labari cewa Sanata Dino Melaye zai sake komawa kan kujerar sa ta ‘Dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Kogi ta yamma. Sanatan ya doke ‘Dan takarar APC a zaben da aka yi shekaran jiya.

2019: Dino Melaya ya doke Smart Adeyami a Kogi ta Yamma
Dino Melaye ya lallasa ‘Dan takarar APC a zaben Majalisa
Asali: UGC

Sanata Dino Melaye ya lallasa ‘Dan takarar APC watau Sanata Smart Adeyami a zaben Majalisar Dattawa na yankin Yammacin Kogi da aka yi a karshen makon jiya. Shi kan sa dai Smart Adeyami tsohon Sanata ne a da karkashin PDP.

Hukumar zabe na kasa na INEC ta tabbatar da sakamakon zaben yankin na Kogi inda aka bayyana Dino Melaye a matsayin wanda yayi nasara. Farfesa Emmanuel Bala wanda shi ne Malamin zaben, ya fitar da sakamakon dazu nan da sassafe.

KU KARANTA: Sakamakon zaben Jihar Filato ya nuna PDP tayi wa APC nisa

Jami’in na INEC, Emmanuel Bala, yake cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 85, 395 a zaben da aka yi, yayin da jam’iyyar APC ta samu kuri’a 66, 901. Wannan ya ba Sanata Dino Melaye na PDP dama a kan Smart Adeyami na jam'iyyar APC.

Haka kuma a zaben ‘dan majalisar wakilai na tarayya na yankin Lokoja da Koto, Alhaji Abdulkarim Isah–Wambai na jam’iyyar APC mai mulki ne yayi nasara. Farfesa Muhammed Suleiman ya bayyana wannan a madadin hukumar INEC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel