Da duminsa: Dogara ya lashe zabe a Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, a karo na hudu

Da duminsa: Dogara ya lashe zabe a Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, a karo na hudu

- Yakubu Dogara ya lashe zaben mazabarsa ta kananan hukumomin Bogoro, Dass da Tafawa Balewa, wanda ya bashi damar komawa majalisar a karo na hudu

- Jami'in hukumar INEC mai tattara sakamako na mazabar, FarfesaAbdulhamid ya bayyana hakan a cibiyar tattara kuri'un mazabar da ke garin Zwall

- Farfesa Abdulhamid ya ce Dogara ya samu kuri'u 73,609, yayin da Dalhatu Ibrahim Kantana na APC ya samu kuri'u 50,780

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu na nuni da cewa kakakin majalisar wakilan tarayya Yakubu Dogara ya lashe zaben mazabarsa ta kananan hukumomin Bogoro, Dass da Tafawa Balewa, wanda ya bashi damar komawa majalisar a karo na hudu.

Jami'in hukumar INEC mai tattara sakamako na mazabar, Farfesa Ahmed Abdulhamid ya bayyana hakan a cibiyar tattara kuri'un mazabar da ke garin Zwall, karamar hukumar Tafawa Balewa, jihar Bauchi.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: PDP ta lallasa APC a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, Bauchi

Da duminsa: Dogara ya lashe zabe a Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, a karo na hudu
Da duminsa: Dogara ya lashe zabe a Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, a karo na hudu
Asali: Twitter

Farfesa Ahmed Abdulhamid ya ce Yakubu Dogara na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u dubu saba'in da ukku da dari shida da tara (73,609) , yayin da Dalhatu Ibrahim Kantana na jam'iyyar APC ya samu kuri'u dubu hamsin da saba'in da takwas (50,780).

A cewarsa, Yakubu Dogara na jam'iyyar PDP wanda ke wakiltar mazabar a majaloisar wakilan tarayya, ya lashe zaben, wanda zai bashi damar komawa majalisar a karo na hudu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel