PDP ta ci kananan hukumomi 5 a Oyo da kuma 9 a cikin Jihar Ondo

PDP ta ci kananan hukumomi 5 a Oyo da kuma 9 a cikin Jihar Ondo

Mun samu labari cewa jam’iyyar adawa ta PDP ce ta samu nasara a Jihohin Oyo da Ondo kamar yadda sakamakon da aka fitar. Bisa dukkan alamu Atiku Abubakar yayi wa Buhari illa a wadannan Yankin na APC.

PDP ta ci kananan hukumomi 5 a Oyo da kuma 9 a cikin Jihar Ondo
Atiku yayi wa Buhari gaba a Jihar Ondo da kuma Oyo
Asali: Facebook

A jihar Oyo, jam'iyyar PDP ce tayi nasara a zaben shugaban kasa kamar yadda sakamakon da aka fitar daga kananan hukumomin jihar irin su Afijio, Saki ta Gabas, Kajola, Ibarapa ta Arewa, Ibarapa ta gabas da kuma karamar hukimar Itesiwaju.

Ma'aikatan INEC sun bayyana cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri'u 366,640 yayin da shi kuma babban abokin hammayar Atiku Abubakar wanda shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, ya samu kuri'u 365,229 a zaben da aka yi.

KU KARANTA: 2019: Ya zabi Shugaba Buhari a Daura daf da zai mutu ya bar Duniya

Haka zalika a Jihar Ondo, PDP ce ta lashe mafi yawan kananan hukumomin jihar a sakamakon da ya bayyana. Atiku Abubakar Abubakar na PDP ya ci kuri'a 275,901. Shi kuma Muhammadu Buhari ona APC ya samu kuri'u 241,769 a Jihar ta APC.

A baya kun ji cewa Atiku ya ci Garuruwan Idanre, Gabashin Ondo, Ose, Ifedore, Akure ta Arewa, Ile Oluji Oke Igbo, Irele sannan kuma da karamar hukumar Okitipupa. APC kuma ta kawo duka kananan hukumomin da ke cikin Akoko Owo daOdigbo

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel