Saraki: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Kwara ta tsakiya

Saraki: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Kwara ta tsakiya

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara ta ki amincewa da sakamakon zabe na dan majalisa na yankin Kwara ta tsakiya da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar

- Jami'in PDP a yankin yaki sanya hannu kan sakamakon zaben

- Yayi zargin cewa anyi masu murdiya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara ta ki amincewa da sakamakon zabe na dan majalisa na yankin Kwara ta tsakiya da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar.

Jami’in jam’iyyar na yankin Kwara ta tsakiya, Hon. Isiaka Magaji yaki sanya hannunsa akan sakamakon zaben daan majalisa na yankin Kwara ta tsakiya, inda yace anyi magudi.

Saraki: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Kwara ta tsakiya
Saraki: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Kwara ta tsakiya
Asali: Depositphotos

Da yake jawabi a lokacin da aka kira wakilan jam’iyyun siyasa domin su fito su sanya hannu kan sakamakon karshe, Hon. Magaji ya bayyana cewa rahoto daga jami’ in PDP na kowace karamar hukuma a Kwara ta tsakiya ya bayyana cewa akwai zamba sosai a zaben.

Daga bisani sai Jami’ in PDP ya gabatar da wata wasikar zanga-zanga ga jami’ in zaben, Farfesa Olawale Olatubosun.

Olatubosun, ya ki amsar wasikar daga hannun magaji, cewa “Baniu da hurumin karban irin wannan wasikar.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya lashe jihar Osun

Don haka sauran jam’ iyyun siyasa irin su APC, LP da AAP sun saanya hannu akan sakamakon.

Shugaban majalisar dattawaa, Dr Bukola Saraki ne dan takarar PDP a yankin Kwara ta tsakiya a zaben ranar Asabar da ya gudana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel