Yanzu Yanzu: Buhari ya lashe jihar Osun

Yanzu Yanzu: Buhari ya lashe jihar Osun

Dan takarar shugaan kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Shugaba Muhammadu Buhari, ya lashe zabe a jihar Osun.

Buhari ya kayar da babban abokin adawarsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben Shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga waatan Fabrairu a jihar Osun sannan Toyin Ogundipe, mataimakin Shugaban jami’ar Lagas ya sanar da hakan.

Shugaba Buhari ya samu kuri’u 347,674 yayinda Atiku ya samu 337,377, hakan yasa aka samu takarar kuri’u 10,297 a tsakaninsu.

Ya lashe kananan hukumomi 18 cikin 30 a jihar yayin Atiku ya lashe 12.

A wani lamari na daban, mun rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fadi a dukkanin kananan hukumomin da ke yankinsa na Kwara ta tsakiya a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

Da farko Legit.ng ta rahoto inda ya fadi a kananan hukumomi uku cikin hudu. Kananan hukumomin sune Asa, Ilorin South da kuma Ilorin East. Na hudun shine Ilorin West, wanda ya kasance ainahin karamar hukumar Shugaban majalisar dattawan.

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa APC ta samu 51, 531 yayinda PDP ta samu 30,075.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel