PDP ta samu kuri’a 248, 000 daga kananan hukumi 8 na Jihar Filato

PDP ta samu kuri’a 248, 000 daga kananan hukumi 8 na Jihar Filato

- Atiku Abubakar yayi nasara a cikin kananan hukumomi 6 na Jihar Filato

- Buhari ya samu kuri’a 138, 268 yayin da Atiku na PDP ya samu 248, 210

PDP ta samu kuri’a 248, 000 daga kananan hukumi 8 na Jihar Filato
An ba Buhari rata a sakamakon zaben Jihar Filato da aka soma fitarwa
Asali: UGC

Mun ji labari cewa ‘dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa watau Alhaji Atiku Abubakar, ne yake kan gaba a sakamakon da ake kirgawa a jihar Filato. Hukumar NAN mai dillacin labarai na kasa ta bayyana mana wannan.

Atiku Abubakar na PDP ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a kananan hukumomi 6 daga cikin 8 da aka sanar da sakamakon su kawo yanzu. Atiku ya samu nasara ne a irin su Bokks, Mikangm Kanke, da kuma Pankshin.

KU KARANTA: Buhari ya sha gaban 'Dan takarar PDP Atiku a Kano

Shi kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iya kawowa kanannan hukumomi 2 ne na jihar watau Jos ta Fabas da kuma Quanpan. Atiku na PDP shi ne wanda ya ci Langtang ta Kudu da kuma Jos ta Kudu a halin yanzu.

A sakamakon da hukumar INEC mai zaman kan ta ta fitar, jam’iyyar adawa ta PDP tana da kuri’a 248, 210. Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC mai mulki kuma yana da kuri’u 138, 268 daga kirgen zaben.

Akwai dai kanannan hukumomi 17 ne a cikin jihar ta Filato da ke cikin Arewa maso tsakiyar Najeriya. Yanzu haka dai ana cigaba da fitar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi Ranar Asabar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel