Albarkacin kaza: Dan yayar Buhari ya yi biji biji da jam’iyyar PDP a takarar dan majalisa

Albarkacin kaza: Dan yayar Buhari ya yi biji biji da jam’iyyar PDP a takarar dan majalisa

Dan yayar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Fatuhu Muhammad ya lashe zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Daura, Sandamu da Maiadua cikin ruwan sanyi, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta bayyana.

Legit.ng ta ruwaito Fatuhu ya tsaya takarar dan majalisar ne a karkashin inuwar jam’iyyar APC ta Baba Buhari, inda ya buga da dan takarar jam’iyyar PDP, Usman Tela, bayan dan majalisa mai ci ya janye masa a yayin zaben fidda gwani.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta musanta batun cafke Buba Galadima

Albarkacin kaza: Dan yayar Buhari ya yi biji biji da jam’iyyar PDP a takarar dan majalisa
Fatuhu Buhari
Asali: UGC

Da yake sanar da sakamakon zaben, baturen zabe na hukumar INEC ya bayyana cewa an kada kuri’u dubu dari da talatin da tara da tari takwas da talatin da bakwai, 139, 837, daga cikinsu akwai kuri’u dubu takwas da dari uku da ashirin da tara, 8,329 da suka lalace.

Ya kara da cewa Fatuhu da jam’iyyarsa ta APC sun samu kuri’u dubu Casa’in da hudu da dari bakwai da talatin da hudu, 94, 734 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu ashirin da biyar da dari da goma sha hudu, 25, 114.

Sai dai wakilin jam’iyyar PDP, Aminu Manzo Daura ya nuna shakkunsa game da alkalumman sakamakon zaben da aka bayyana, inda yace akwai matsaloli dake tattare da sakamakon zaben da INEC ta bayyana.

Malam Fatuhu Muhammed yayi karatun boko, inda har ya samu digiri a sha’anin kimiyyar siyasa daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, kuma ya taba yin aiki a hukumar kula da hanyoyin ruwan Najeriya, NIMASA da kuma hukumar kula da kamfanonin sadarwa, NCC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel