Hukumar DSS ta musanta batun cafke Buba Galadima

Hukumar DSS ta musanta batun cafke Buba Galadima

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta musanta rahoton da ake yadawa na cewa wai jami’anta sun cafke fitaccen dan adawan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Injiniya Buba Galadima, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Legit.ng ta ruwaito DSS ta musanta rahoton ne a daren Lahadi, 24 ga watan Feburairu, inda tace ba kamar yadda ake yamadidi a kafafen watsa labaru na ciki da wajen kasar nan ba, bata san ma inda Buba Galadima yake ba.

KU KARANTA: Zaben 2019: Shugaba Buhari ya lallasa Atiku a kananan hukumomi 11 na jihar Kano

A jiya ne aka ruwaito guda cikin yayan Buba Galadima ta bayyana cewa wasu mutane cikin wata mota mara lamba sun cafke mahaifinta a unguwar Wuse 2 na garin Abuja, inda suka yi awon gaba dashi, don haka tayi zargin gwamnati ce ta kama shi.

A ranar Lahadin ne dai kaakakin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Festus Keyamo ya bayyana bukatar ganin an kama Buba Galadima don kada ya kawo tashin hankali a Najeriya sakamakon wani bidiyo da yayi inda yayi zargin PDP ce kan gaba a zaben daya gudana a ranar Asabar.

Sai dai ko a lokacin da Buba yake wannan magana, hukumar INEC bata sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a kowacce jaha ba, don haka APC ta zargi Buba Galadima da shirya makarkashiya tare da shirin tunzura jama’a su ki amincewa da sakamakon zaben idan har ba PDP aka sanar ta ci ba.

A jawabin Keyamo, “Mun samu labarin cewa PDP sun shirya tayar da hankali tare da jefa yan Najeriya cikin rudani ne kafin hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben, don su nuna cewa Atiku ne ya samu nasara tun ma kafin a sanar.

“Daga nan kuma sais u fita da sunan shirya zanga zanga a wasu sassan kasar nan tare da yan daban siyasa da nufin janyo hankalin kasashen duniya domin su tausaya musu, don ganin kasashen duniya sun yi ma Najeriya abinda suka yi ma kasar Venezuela.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel