Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah ya sha kashi a hannun Lola Ashiru

Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah ya sha kashi a hannun Lola Ashiru

Gwamnan jihar Kwara, Ahmed Abdulfatah ya fadi zaben kujeran sanata na yankin Kwara ta kudu a zaben da ya gudana a jiya Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da Lola Ashiru a matsayin Sanatan Kwara ta kudu.

Jam’iyyar APC ta lashe kananan hukumomi shida cikin bakwai da ke yankin Kwara ta kudu.

Kananan hukumomin sune: Ekiti, Ifelodun, Irepodun, Isin, Offa, Oke-Ero, da kuma Oyun.

Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah ya sha kashi a hannun Lola Ashiru
Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah ya sha kashi a hannun Lola Ashiru
Asali: UGC

A karamar hukumar Ekiti, APC na da 6807 yayinda PDP ke da 5,538, sannan a karamar hukumar Ifelodun APC na da 20,026 yayinda PDP ke da 9,180.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

A karamar hukumar Irepodun kuma APC na da 14,967 yayinda PDP ke da 10,417, a karamar hukumar Isin kuma APC na da 6,064 yayinda PDP ta samu 4,141, a karamar hukumar Offa APC ta samu 24,279 inda PDP ta samu 4,443, a Oke-Ero APC na da 6,186 inda PDP ke da 6,444, daga karshe a karamar hukumar Oyun APC na da 11,388 inda PDP ta samu 4,971.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel