Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a dukkanin kananan hukumomi 4 na yankinsa

Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a dukkanin kananan hukumomi 4 na yankinsa

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fadi a dukkanin kananan hukumomin da ke yankinsa na Kwara ta tsakiya a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

Da farko Legit.ng ta rahoto inda ya fadi a kananan hukumomi uku cikin hudu.

Kananan hukumomin sune Asa, Ilorin South da kuma Ilorin East. Na hudun shine Ilorin West, wanda ya kasance ainahin karamar hukumar Shugaban majalisar dattawan.

Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a dukkanin kananan hukumomi 4 na yankinsa
Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a dukkanin kananan hukumomi 4 na yankinsa
Asali: Depositphotos

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa APC ta samu 51, 531 yayinda PDP ta samu 30,075.

Yawan masu rijista ya kasance 224, 494, yayinda wadanda aka tantance ya kama 91,130.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel