Zaben 2019: Gwamna Ganduje ya fidda Buhari kunya a karamar hukumar Dawakin Tofa

Zaben 2019: Gwamna Ganduje ya fidda Buhari kunya a karamar hukumar Dawakin Tofa

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun tabbatar da cewa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya fidda kansa kunya da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayin da jam'iyyar su ta APC ta yi nasara a karamar hukumar Dawakin Tofa da ke jihar Kano.

A yayin babban zaben kasa da aka gudanar a jiya Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mun samu cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya fidda shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya yayin da ya tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Zaben 2019: Gwamna Ganduje ya fidda Buhari kunya a karamar hukumar Dawakin Tofa
Zaben 2019: Gwamna Ganduje ya fidda Buhari kunya a karamar hukumar Dawakin Tofa
Asali: Facebook

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kasancewar ta mahaifar sa, Gwamna Ganduje bai yi sake ba wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa inda shugaban kasa Buhari ya yi nasara da kimanin kuri'u 37,147.

Ko shakka ba bu shugaban kasa Buhari ya lallasa babban abokin adawar sa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ya samu kuri'u 6,507 kacal a mahaifar gwamna mai ci a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu, shugaban kasa Buhari ya yiwa Atiku nisan gaske wanda ba zai ji kira ba yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fara fidda sakamakon yadda zaben ya kaya a wasu kananan hukumomi na Kanon Dabo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel