Yanzu-yanzu: Saraki ya fadi warwas, ba zai koma majalisa ba

Yanzu-yanzu: Saraki ya fadi warwas, ba zai koma majalisa ba

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya fadi a takarar zabensa na kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar Kwara ta tsakiya a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Saraki, na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya lallasu ne hannun Dakta Ibrahim Yahya Oloriegbe na jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Ibrahim Yahaya ya doke Saraki a dukkan kananan hukumomi hudu na mazabar Kwara ta tsakiya. ga sakamakon zaben:

Ilori ta yamma

APC - 51,531

PDP - 30,075

Ilori ta kudu

APC - 26,331

PDP- 13,013

Ilori ta gabas

APC- 30,014

PDP - 14,654

Asa

APC - 15,932

PDP - 11,252

A bayan mun kawo muku rahoton cewa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC yana kan gaba a kananan hukumomi 9 na jihar Kwara, yayinda Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ke biye da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel