Hukumar INEC ta fara sanar da sakamakon zaben 2019 daga birnin Ilorin

Hukumar INEC ta fara sanar da sakamakon zaben 2019 daga birnin Ilorin

Mun samu cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta fara bayar da sanarwa dangane da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar cikin duk wani kwararo, lungu da kuma sako da ke fadin kasar nan a jiya Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

A yayin da hukumar zabe ta kasa ta dugunzuma haikan wajen sanar da sakamakon babban zabe, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, ya yi shigar fari inda a halin yanzu ya ke kan gaba ta fuskar nasara a jihar Kwara.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya na kan gaba yayin da ofishin hukumar INEC da ke Ilorin ya bayar da tabbacin nasarar sa bayan kammala tantance sakamakon zaben kananan hukumomi 7 na jihar Kwara.

Hukumar INEC ta fara sanar da sakamakon zaben 2019 daga birnin Ilorin
Hukumar INEC ta fara sanar da sakamakon zaben 2019 daga birnin Ilorin
Asali: Twitter

Ga yadda sakamakon zaben ya kaya cikin kananan hukumomin bakwai kamar yadda INEC ta wassafa inda jam'iyyar APC ke da kuri'u 11, 051 yayin da PDP ta samu kuri'u 4,904 a karamar hukumar Oyun; APC ta samu kuri'u 6,079 yayin da PDP ta samu kuri'u 6,242 a karamar hukumar Oke-Ero.

A karamar hukumar Ekiti; APC ta samu kuri'u 6,662 yayin da PDP ta lashe kuri'u 5,397. APC ta samu kuri'u 15,976 yayin da PDP ta samu kuri'u 10,709 a karamar hukumar Asa. Cikin karamar hukumar Irepodun kuma, jam'iyyar APC ta samu kuri'u 14,395 yayin da PDP ta samu kuri'u 10,232.

Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 17,534 yayin da PDP ta samu kuri'u 7,598 a karamar hukumar Mooro. Kazalika APC ta samu jimillar kuri'u 31,039 yayin da PDP ta samu kuri'u 12,820 a shiyyar Ilorin ta Gabas.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jimillar kuri'u kamar yadda hukumar INEC ta bayyana daga birnin Ilorin, jam'iyyar APC ta samu kuri'u 102,736 yayin da PDP ta samu kuri'u 57,898 cikin kananan hukumomi bakwai na jihar Kwara.

A yayin da hukumar ke ci gaba da kirdadon sakamakon zaben sauran kananan hukumomin 9 da ke fadin jihar Kwara, a halin yanzu shugaban kasa Buhari ya ja ragama ta kimanin kuri'u 44,838 doriya akan na babban abokin hamayyar sa dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel