2019: Wani Matashi ya mutu awanni bayan ya dangwalawa APC

2019: Wani Matashi ya mutu awanni bayan ya dangwalawa APC

Mun samu labari cewa wani mutumi ya rasu jim kadan bayan ya dangwalawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’a a akwatin zaben sa da ke Unguwar Sarkin Yara a Garin Daura da ke Katsina.

2019: Wani Matashi ya mutu awanni bayan ya dangwalawa APC
Maras lafiya ya cika karfe 6:30 bayan ya kadawa Buhari kuri’a
Asali: Facebook

Wani Matashi mai suna Bashir Mamman Tela ya rasu ne bayan ya kadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC kuri’a a yankin sa na Unguwar Kofar Baru da ke cikin karamar hukumar Daura a jihar Katsina a jiya.

Mahaifin wannan yaro mai suna Alhaji Mamman Tela ya fadawa manema labarai cewa yaron na sa ya rasu na sa’o’i kadan bayan da ya zabi Buhari. Dattijon yace dama can yaron ya dade yana fama da rashin lafiya tun tuni.

KU KARANTA: Labarin yadda Atiku da Shugaba Buhari su ke gwabzawa a Katsina

Tela yace Saurayin ya shafe akalla shekaru 3 yana rashin lafiya, tun bayan da ya kamalla karatun Sakandare. Alhaji Tela yake cewa bangaren jikin wannan saurayi ya shanye a 2016 wanda a karshen tayi sanadiyyar ajalin sa.

Alhaji Tela ya bayyanawa ‘yan jaridar Daily Trust cewa an yi dace yaron ya iya zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce a kan karagar mulki kafin ya bar Duniya jiya Asabar da yamma da karfe 6:30.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel