Yanzu Yanzu: APC ta nemi ayi gaggawan kama Buba Galadima

Yanzu Yanzu: APC ta nemi ayi gaggawan kama Buba Galadima

Kungiyar kamfen din Shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi kira ga ayi gaggawan kama Buba Galadima, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wata sanarwa a ranar Lahadi, kungiyar kamfen din APC ta zargi Galadima da makircin kaddamar da Atiku Aubakar na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa.

Kungiyar tayi ikirarin cewa Galadima yayi wani dan gajeren bidiyo akan haka, yayinda yake a matsayin kakakin kungiyar kamfen din PDP.

Ta kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar adawa na shirin kwasan yan iska don yin zanga-zangan kasa baki daya.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

A halin da ake ciki, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kan gaba a yanzu haka yayinda INEC ke ci gaba da hada sakamakon zabe na jihar Kwara, APC na da 11,051 inda PDP ke da 4,904 daga karamar hukumar Oyun.

Hakazalika APC na da 6,079 yayinda PDP ke da 6,242 a karamar hukumar Oke-Ero. Sannan APC na da 6,662 yayinda PDP ke da 5,397 a karamar hukumar Ekiti. A Asa, APC na da 15,976, yayinda PDP ta samu 10,705.

A Irepodun, APC na da 14,395, PDP na da 10,232. A Karamar hukumar Mooro na da APC scored 17,534 sannan PDP na da 7,598. A Ilorin East, APC ta tashi da kuri’u 31,039 sannan PDP ta samu 12,820.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel