Yanzu-yanzu: An damke Buba Galadima

Yanzu-yanzu: An damke Buba Galadima

Jami'an tsaro sun damke kakakin yakin neman zaben jam'iyyar Peoples Democratic Party, Injinya Buba Galadima, a ranan Lahadi, 24 ga watan Febrairu, 2019.

Rahoto daga jaridar DAILY NIGERIAN ta bayan cewa daya daga cikin 'yayan Buba Galadima ta tabbatarwa manema labarai cewa jami'an tsaro sun damke mahaifinta a unguwar Wuse 2 dake birnin tarayya Abuja.

Mun kawo muku cewa Kungiyar kamfen din Shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi kira ga ayi gaggawan kama Buba Galadima, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wata sanarwa a ranar Lahadi, kungiyar kamfen din APC ta zargi Galadima da makircin kaddamar da Atiku Aubakar na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa.

Kungiyar tayi ikirarin cewa Galadima yayi wani dan gajeren bidiyo akan haka, yayinda yake a matsayin kakakin kungiyar kamfen din PDP.

Ta kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar adawa na shirin kwasan yan iska don yin zanga-zangan kasa baki daya.

Ku saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel