Kwankwaso ya gaza, Buhari ya lallasa Atiku a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano

Kwankwaso ya gaza, Buhari ya lallasa Atiku a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, jam'iyyar APC ta yi nasara a babban zaben kujerar shugaban kasa, majalisar dattawa da kuma ta majalisar wakilai da aka gudanar cikin karamar hukumar Madobi ta jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC, ya lallasa babban abokin adawar sa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a karamar hukumar Madobi da ta kasance mahaifa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso.

Masu sharhi sun bayyana cewa, Kwankwaso ya gaza fidda kansa kunya a garin Madobi duk da kasancewar sa babban jagora na jam'iyyar PDP a jihar Kano kuma daya daga cikin jiga-jigan kungiyar yakin neman zaben Atiku.

Kwankwaso ya gaza, Buhari ya lallasa Atiku a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano
Kwankwaso ya gaza, Buhari ya lallasa Atiku a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano
Asali: Twitter

Yayin zayyana sakamakon zaben a yau Lahadi cikin karamar hukumar Madobi, alkalin zaben, Sani Umar, ya bayar da shaidar cewa akwai adadi masu rajistar zabe kimanin 84,067 yayin da a ranar zabe aka tantance masu niyyar kada kuri'u 40,764 kacal.

Jami'in na hukumar zabe ta kasa cikin jawaban sa ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar APC a zaben kujerar shugaban kasa cikin karamar hukumar Madobi da aka gudanar a ranar Asabar ta lashe kimanin kuri'u 26,110 yayin da jam'iyyar PDP ta lashe kuri'u 13,113 kacal.

KU KARANTA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

A yayin zaben kujerar majalisar dattawa kuma, jam'iyyar APC ta yi nasara da kimanin kuri'u 22,731 yayin da jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe kuri'u 15,913.

Sai ba bu shakka jam'iyyar PDP ta yi nasara a akwatin mazabar Kwankwaso inda rahotanni suka bayyana cewa Atiku samu kuri'u 278 yayin da Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 215.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel