Yanzu-yanzu: Buhari ya lallasa Atiku a jihar Ekiti

Yanzu-yanzu: Buhari ya lallasa Atiku a jihar Ekiti

Shugaba Muhammadu Buhari ya lallasa abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, a jihar Ekiti. Jiha ta farko da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa an kammala 'kirgan kuri'u.

A natijan zaben da alkalain zaben jihar, Farfesa Idowu Olayinka, shugaba jami'ar Ibadan ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress ya samu kuri'u 219,231 yayinda Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya samu kuri'u 154,032.

Mun kawo muku cewa Jam'iyyar All Progressives Congress, APC ta lashe dukkan kujerun majalisar dattawan tarayya uku da majalisar wakilai biyu a zaben da aka gudanar ranan Asabar, 24 ga watan Febrairu, 2019.

A sakamakon da Alkalin zaben kudancin Ekiti, Farfesa Laide Lawal, ya ce Prince Dayo Adeyeye na APC ya samu kuri'u 77,621 inda abokiyar hamayyarsa, Sanata Biodun Olujimi ya samu kuri'u 53,741.

A yankin arewacin Ekiti, alkalain zaben, farfesa Fasina Abayomi, ya alanta Olubunmi Adetunbi na jam'iyyar APC a matsayin zakara inda ya smau kuri'u 60,689 yayinda Sanata Duro Faseyi na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 49,209.

A yankin Ekiti ta tsakiya kuwa, Bamidele ya kayar da dan takaran jam'iyyar PDP

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel