Zaben 2019: Nan ba da jimawa ba za mu sanar da shugaban kasar Nigeria na gaba - INEC

Zaben 2019: Nan ba da jimawa ba za mu sanar da shugaban kasar Nigeria na gaba - INEC

- INEC ta ce nan ba da jimawa ba zata sanar da shugaban kasar Nigeria na gaba, wanda zai mulki kasar daga 2019 zuwa 2023

- Yakubu ya bayyana gamsuwarka kan yadda zaben ya gudana amma ya ce an samu matsaloli a wasu sassa na kasar, musamman jihohin Legas, Imo da Abuja

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce nan ba da jimawa ba zata sanar da shugaban kasar Nigeria na gaba, wanda zai mulki kasar daga 2019 zuwa 2023.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar INEC, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Lahadi a karshen wata ganawa da manema labarai dangane da halin da kasar ke ciki bayan kammala zaben kasar a ranar Asabar.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Zaben 2019: Nan ba da jimawa ba za mu sanar da shugaban kasar Nigeria na gaba - INEC
Zaben 2019: Nan ba da jimawa ba za mu sanar da shugaban kasar Nigeria na gaba - INEC
Asali: Original

Yakubu ya bayyana gamsuwarka kan yadda zaben ya gudana amma ya ce an samu matsaloli a wasu sassa na kasar, musamman jihohin Legas, Imo da Abuja.

Bayan nan, ya ce: "Aiki ya ci gaba; ina gayyatarku 'yan jarida, da misalin karfe 6 na yamma, mu hadu a cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa.

"Zamu kaddamar da fara tattara sakamakon zaben jihohi 36 da na birnin tarayya Abuja, muna sa ran nan ba da jimawa ba zamu sanar da shugaban kasar na nan gaba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel