Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a daya daga cikin kananan hukumomi 4

Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a daya daga cikin kananan hukumomi 4

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya fadi a daya daga cikin kananan hukumomi hudu a yankin Kwara ta tsakiya a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Mista Saraki dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sha kaye a hannun Ibrahim Oloriegbe na APC.

Akwai kananan hukumomi hudu a yankin wanda suka hada da Asa, Ilorin West, Ilorin East da kuma Ilorin South.

Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a daya daga cikin kananan hukumomi 4
Yanzu Yanzu: Saraki ya sha kaye a daya daga cikin kananan hukumomi 4
Asali: UGC

Yayinda hukumar zabe ke sanar da sakamako a ofishin INEC a ranar Lahadi a karamar hukumar Asa, Mista Saraki na ya samu kuri’u 11, 252, yayinda dan takarar APC ya samu 15,932.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

Jami’in zabe ya bayar da adadin masu rijista a matsayin 73,425, yayinda aka tantance masu zabe 29,023.

Ana jiran sakamako daga sauran kananan hukumomi ukun a lokacin wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel