Yanzu yanzu: INEC na ci gaba da gudanar da zabe a mazabar Yakubu Dogara

Yanzu yanzu: INEC na ci gaba da gudanar da zabe a mazabar Yakubu Dogara

- INEC na ci gaba da sake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, jihar Bauchi

- INEC ta ce tana sake gudanar da zaben ne sakamakon lalacewar na'urorin tantance masu zabe a jiya Asabar.

- Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa tun wajen karfe 10:45 na safiyar yau Lahadi, jami'an tsaro da na hukumar zabe sun isa gundumar Lere domin gudanar da zaben

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na ci gaba da sake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a rumfunan zabe na garin Kofti, mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, jihar Bauchi, sakamakon lalacewar na'urar tantance masu kad'a kuri'a.

A halin yanzu, kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, shi ke wakiltar mazabar a majalisar wakilan tarayya, wanda kuma ke neman tazarce a karo na hudu, karkashina jam'iyyar PDP.

A cewar jami'an INEC da ke cibiyar tattara kuri'un mazabar da ke garin Zwall, an sake gudanar da zaben ne na rumfar zaben garin Kofti, bayan da na'urorin tantance masu zabe suka gaza yin aiki har bayan karfe 2 na ranar Asabar.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Yanzu yanzu: INEC na ci gaba da gudanar da zabe a mazabar Yakubu Dogara
Yanzu yanzu: INEC na ci gaba da gudanar da zabe a mazabar Yakubu Dogara
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa tun wajen karfe 10:45 na safiyar yau Lahadi, jami'an tsaro da na hukumar zabe sun isa gundumar Lere domin gudanar da zaben.

A wani labarin, ana ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka kad'a a kananan hukumo ukku na mazabar. Har zuwa karfe 12 na rana, jami'an zabe da ke cibiyar tattara kuri'un, sun ce har yanzu suna kan dakon isowar sakamakon zabe daga kauyukan da ke nesa da cikin garuruwan, musamman garuruwan da ke fuskantar zanga zanga.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel