2019: Har yanzu mutane na cigaba kada kuri’a a Jihar Zamfara

2019: Har yanzu mutane na cigaba kada kuri’a a Jihar Zamfara

Mu na samun labari cewa ana cigaba da zabe a rumfuna 77 a cikin kananan hukumomi 10 na jihar Zamfara. Wani babban jami’in hukumar zabe na INEC na kasa ne ya bayyanawa Daily Trust wannan.

Garba Galadima wanda shi ne shugaban sashen da ke kula da harkar wayar da kan jama’a da kuma yada labarai a hukumar zabe mai zaman kan-ta, ya fadawa ‘yan jarida cewa za a cigaba da zabe a cikin jihar Zamfara har zuwa yau.

An bada dama a cigaba da gudanar da zabe ne a yau Ranar Lahadi a sakamakon ta’addancin wasu miyagu da kuma makara da aka yi wajen fara zabe a jihar. An kuma yi ta fama da na’urorin tantance masu kada zabe a jihar.

KU KARANTA: Rikicin Magoya bayan ‘yan siyasa ya ci mutane 3

Wannan ne dai su ka so dole hukumar INEC ta bada dama a cigaba da kada kuri’a a zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar tarayya na wakilai da dattawa. Wannan matsala dai ta shafi kananan hukumo 10 ne kurum na Zamfara.

Babban jami’in na hukumar INEC ya kuma bayyana cewa an kammala zabe a wasu kananan hukumomi 4 na cikin jihar ta Zamfara. An samu barazanar tsaro a yankin wanda ya sa INEC ta maida zaben zuwa wasu wuraren na dabam.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel