Yanzu-yanzu: APC ta lashe kujeran sanata 2 a jihar Ekiti

Yanzu-yanzu: APC ta lashe kujeran sanata 2 a jihar Ekiti

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC ta lashe kujerun majalisar dattawa biyu da majalisar wakilai biyu a zaben da aka gudanar ranan Asabar, 24 ga watan Febrairu, 2019.

A sakamakon da Alkalin zaben kudancin Ekiti, Farfesa Laide Lawal, ya ce Prince Dayo Adeyeye na APC ya samu kuri'u 77,621 inda abokiyar hamayyarsa, Sanata Biodun Olujimi ya samu kuri'u 53,741.

A yankin arewacin Ekiti, alkalain zaben, farfesa Fasina Abayomi, ya alanta Olubunmi Adetunbi na jam'iyyar APC a matsayin zakara inda ya smau kuri'u 60,689 yayinda Sanata Duro Faseyi na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 49,209.

KU KARANTA: Atiku ya koma Abuja

Hakazalika, alkalain zaben majalisar wakilai ya alanta Yemi Adaramodu na jam'iyyar APC ya lashe kujeran mazabar Ekiti ta kudu inda ya samu kuri'u 41,864 yayinda abokin hamayyarsa Segun Adekola na PDP ya samu kuri'u 25,707.

Sannan a mazabar majalisar wakilan Ekiti North 2 Olanrewaju Ibrahim na jam'iyyar APC ya lashe zaben da kuri'u 29,388 inda ya lallasa Olusola Omotosho na PDP wada ya samu kuri'u 23,684.

Har yanzu ana sauraron mazabar Sanata tsakiyar Ekiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel