Buhari, Shettima sun yi nasara a mazabar fadar gwamnatin jihar Borno

Buhari, Shettima sun yi nasara a mazabar fadar gwamnatin jihar Borno

Mun samu cewa, a yayin da a jiya Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, s aka gudanar da babban zabe kasahugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa abokin hamayyarsa Atiku Abubakar, mugunyar kayi a mazabar fadar gwamnatin jihar Borno.

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya lallasa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a mazabar fadar gwamnatin jihar Borno.

Gwamna Kashim Shettima tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Gwamna Kashim Shettima tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Depositphotos

Kazalika majiayar rahoton ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya yi nasara a akwatunan zabe da ke mazabar fadar gwamnatin sa yayin da ya ke hankoron kujerar Sanatan shiyyar Borno ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan kasar nan.

Gwamna Shettima na jam'iyyar APC wanda samu kuri'u 608, ya lallasa babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Muhammad Abba Aji, wanda ya tashi da kuri'u 56 kacal kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

A yayin da sakamakon babban zaben ke ci gaba da bayyana, shugaban kasa Buhari ya samu kimanin kuri'u 585, wanda lallasa babban akokin adawar sa tsohon mataimakin shugaban kasa da ya samu kuri'u 108 kacal a rumfunan zabe da ke fadar gwamnatin Borno.

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Cikin wani rahoton mai babbar alaka ta kusa ba ta nesa ba da wannan rahoto, shugaban kasa Buhari ya samu kuri'u 593 a rumfunan zabe na 4 da kuma na biyar da ke unguwar Bale Galtimari Jere a birnin Maiduguri.

Ko shakka ba bu Atiku wanda samu kuri'u 67 kacal ya sha mugunyar kayi a wannan mazaba yayin da Buhari ya yi masa wucin kece raini na zarra da kuma nuna fifikon magoya baya masu dangwala kuri'a.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel