Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe

Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe

- Wasu yan bindiga sun kai hari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Oriade da ke jihar Osun

- Yan bindigan sun kai harin bazata ne ofishin, inda suka yi ta hari a ofishin hukumar sannan suka lalata wasu kayayyaki mallakarta

Hukumomi sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun kai hari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Oriade da ke jihar Osun da misalin karfe 3:00 na tsakar daren ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Yan bindigan sun kai harin bazata ne ofishin, inda suka yi ta hari a ofishin hukumar sannan suka lalata wasu kayayyaki mallakarta.

Wasu daga cikin abubuwan da aka lalata sun hada da takardun zabe da akwatunan zabe da aka kona da kuma janareto biyu.

Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe
Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe
Asali: UGC

Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe
Yadda yan bindigan suka lalata ginin ofishin INEC din
Asali: UGC

Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe
Yan bindiga na ta harbi a ofishin hukumar ta INEC
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

Yan bindiga sun kai hari ofishin INEC, sun kona kayayyakin zabe
Kayayyakin zabe da aka cinna wa wuta
Asali: UGC

A baya mun samu rahoton cewa an kone wasu akwatunan zabe da ake dangwale a rumfar zabe mai lamba 18 da ke mahadar Ohafia/Ago Palace way a karamar hukumar Oshodi/Isolo da ke jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito wutar da shafi wasu akwatunan zabe da ke rumfar zabe mai lamba 23 a Baba-Ewe Street/Ago Place way. Jami'an wucin gadi na INEC da masu al'umma da suka zo kada kuri'a duk sun tsere domin tsira da lafiyarsu da rayuwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel