Na faruwa yanzu: Zabe na ci gaba da gudana a wasu rumfunan zabe guda 4 a Filato

Na faruwa yanzu: Zabe na ci gaba da gudana a wasu rumfunan zabe guda 4 a Filato

- Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa an soma kad'a kuri'a a wasu rumdunan zabe guda hudu da ke jihar Filato

- An dage zabe a wasu rumfunan zabe guda biyu a garin Attakar, sai wata rumfar a Zawan B Ward da kuma garin Dadin-Kowa, Riyom da kuma karamar hukumar Jos ta Kudu

- An dage zaben ne sakamakon rashin isowar kayan zabe da jami'an zaben akan lokaci

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa an soma kad'a kuri'a a wasu rumdunan zabe guda hudu da ke jihar Filato, biyo bayan dage zaben da aka yi a ranar Asabar sakamakon wasu matsaloli da hukumar zaben kasa INEC ta fuskanta a rumfunan zaben.

Mr. Osaretin Imahireogbo, shugaban sashen ilimantar da masu kad'a kuri'a da hulda da jama'a na hukumar zaben kasa INEC na jihar Filato ya bayyana hakan ga manema labarai a safiyar ranar Lahadi a Jos, birnin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa an dage zabe a wasu rumfunan zabe guda biyu a garin Attakar, sai wata rumfar a Zawan B Ward da kuma wata a garin Dadin-Kowa, Riyom da kuma karamar hukumar Jos ta Kudu.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Yadda Yakubu Dogara ya kawowa Atiku kuri'ar akwatin zabensa

Na faruwa yanzu: Zabe na ci gaba da gudana a wasu rumfunan zabe guda 4 a Filato
Na faruwa yanzu: Zabe na ci gaba da gudana a wasu rumfunan zabe guda 4 a Filato
Asali: Depositphotos

An dage zaben ne sakamakon rashin isowar kayan zabe da jami'an zaben akan lokaci.

"An dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayyha a wasu rumfunan zabe na kanan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu sakamakon tsaikon zuwan malaman zabe da kayan zabe.

"Amma a yanzu haka da na ke maku magana, an soma gudanar da zabukan a wadannan rumfunan zabe da abun ya shafa," a cewar Imahireogbo.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel