An cafke miyagu 4 da nau'rar tantance masu kada kuri'a a jihar Kano

An cafke miyagu 4 da nau'rar tantance masu kada kuri'a a jihar Kano

Mun samu cewa, hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu miyagun mutane hudu dauke da na'urar tantance katin zabe ta Card Reader yayin zaben kasa da aka gudanar a jiya Asabar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, A jiya Asabar, hukumar jami'an 'yan sanda reshen jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu miyagu hudu dauke da na'urar tantance katin zabe har guda takwas yayin zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sabon Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Haruna Abdullahi, shine ya bayar da tabbacin wannan wawan kamu da hukumar ta yi yayin ganawar sa da manema labarai a cikin Kanon Dabo.

An cafke miyagu 4 da nau'rar tantance masu kada kuri'a a jihar Kano
An cafke miyagu 4 da nau'rar tantance masu kada kuri'a a jihar Kano
Asali: Facebook

Abdullahi ya bayyana cewa, miyagun hudu sun shiga hannu a yankin unguwar Sabon Gari da ke tantagwaryar birnin Kano inda a halin yanzu suke ci gaba da bai duga-dugan su hutu a babban ofishin 'yan sanda na CID domin tsananta bincike a kansu.

Babban jami'in 'yan sandan ya kuma bayyana cewa, hukumar ta cafke wasu miyagu hudu yayin yunkurin su na arcewa da akwatunan zabe bayan mummunan ta'annati da suka yiwa kayayyakin zabe a jiya Asabar.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Bisa ga fahimta ta shafin jaridar Legit.ng, majiyar rahoton ta bayyana cewa, wannan abun takaici ya auku ne a daya daga cikin rumfunan zabe na kauyen Takalmawa da ke karkashin hukumar Gabasawa a wajen garin Kano.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, bayan gudanar da babban zabe kasa a jiya Asabar, a yau Lahadin sakamakon yada ta kaya cikin wasu rumfuna da mazabu ya fara bayyana a kafofin watsa labarai da dandalan sada zumunta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel