Ku amince da sakamakon zabe - Obasanjo ya roki 'yan takarar APC da PDP

Ku amince da sakamakon zabe - Obasanjo ya roki 'yan takarar APC da PDP

- Olusegun Obasanjo ya shawarci wadanda suka samu nasara a zabukan shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya da su amince da sakamakon zabe

- Obasanjo ya yi nuni da cewa a kowacce gasa, dole a samu masu nasara da masu faduwa. Wannan shine shirin da kowanne mai gasa ya kamata ya yi

- Jim kadan bayan kad'a kuri'arsa, ya bayyana cewa zaben yana gudana bisa tsari

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shawarci wadanda suka samu nasara a zabukan shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya da su nuna dattako a nasarar da suka samu, yana mai cewa wadanda suka sha kasa ma su amince da shan kayi ba tare da turjiya ba.

Tsohon shugaban kasar ya ce, "a kowacce gasa, dole a samu masu nasara da masu faduwa. Wannan shine shirin da kowanne mai gasa ya kamata ya yi. Wanda duk ya samu nasara, to ya nuna dattako. Idan na sha kasa kuwa, zan hakura in amince da shan kaye. Wannan shine ya kamata a yi a kowacce gasa.

"Idan burinka na shiga kowacce gasa shine ka yi nasara ta kowanne hali, to kuwa wannan ba gasa kake yi ba. Na san cewa INEC za ta sabunta matakan zabenta kafin zuwan sauran zabukan."

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Ku amince da sakamakon zabe - Obasanjo ya roki 'yan takarar APC da PDP
Ku amince da sakamakon zabe - Obasanjo ya roki 'yan takarar APC da PDP
Asali: UGC

Obasanjo ya isa akwatin zabensa da ke gunduma ta 11, akwati na 22, da ke Olusomi, kan titin Totoro, Sokori, karamar Abeokuta ta Arewa, a cikin wata bakar mota kirar Lexus Jeep, mai lamba AAD 24 TF (Ogun), da misalin karfe 11:10 na safe, inda ya kad'a kuri'arsa da misalin karfe 11:15 na safe.

Sai dai, da ya ke tsokaci kan wahalar da ya sha kafin ya kad'a kuri'ar ta sa, ya ce: "Na zo nan ne domin kad'a kuri'ata. Ina da yakinin cewa an samu tsaiko a mazaba ta.

"An kawo kayayyakin zaben a kurarren lokaci. Kusan an samu lattin awanni uku, wanda hakan ma za a iya magancewa. Baicin wannan, komai na tafiya yadda ya kamata.

"Na hau layi an kuma tantance ni. Sai dai sun samu matsala a lokacin da zan dora yatsan hannuna domin na'urar ta tantance ni, sai da aka dan sha daga kafin nan na'urar ta tantance ni, inda kuma suka yi mun jagora har na kad'a kuri'ata."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel